Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe shugaban yan ta’adda tare da kwato bindigogin yaƙi a Katsina

Published

on

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kashe wani babban kwamandan ’yan ta’adda tare da kwato bindigogi da alburusai da babura a yayin wani samame a ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

A cewar wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Joint Task Force, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Lahadi, sojojin sun gudanar da aikin ne a ranar 29 ga Agusta, 2026, inda suka yi arangama da ’yan ta’addan da suka yi musu tsayin daka kafin sojojin su tilasta musu tserewa.

Sojojin sun tabbatar da kashe wani ɗan ta’adda da aka bayyana da suna Smally, wanda aka ce Laftanar ne a ƙarƙashin fitaccen shugaban ’yan ta’adda Kachalla Muhammadu Filani.

Rundunar ta ce ta kuma kwato bindigogin mashin guda uku, AK-47 guda biyu, harsashi masu tarin yawa, da babura guda shida da ake zargin ’yan ta’addan ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Rundunar ta ƙara da cewa aikin wani ɓangare ne na ci gaba da kai hare-hare domin matsa wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda lamba tare da tarwatsa ƙarfin gudanar da ayyukansu a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!