Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Yan wasa 124 ne zasu fafata a gasar Tennis ta Dala Hard Court a Kano

Published

on

Akalla ‘yan wasa 124, ne ake sa ran zasu fafata a gasar Kwallon Tennis ta Dala Hard Court , da zata gudana a birnin Kano Najeriya daga ranar Jumma’a 29 zuwa Lahadi 06 ga watan Nuwamba 2021.

Shugaban gudanar da gasar Alhaji Yusuf Datti , ne ya bayyana haka ga ‘yan Jaridu a wani taro da ya gudana na sanar da tsarin yadda gasar zata gudana , a harabar filin wasan Tennis dake Club Road.

Kano Pillars za ta dawo filin wasanta na Ƙofar Mata – LMC

Datti ya kara dacewa gasar wacce zata gudana karo na 34, ta gayyaci ‘yan wasa 20 Maza kwararru da Mata 10 suma kwararru ,zuwa raba Jadawalin gasar inda a gefe daya kuma za’a gudanar da wasan Neman cancanta na Preliminary ga matsakaitan ‘yan wasa daga ranar 29 ga Oktoba zuwa 01 ga Nuwamba.

” Kudin gudanar da gasar a bana yana nan yadda aka san shi, inda zamu bada kyautar Naira Miliyan Daya ga Zakara a bangaren Maza, ya yinda zamu bada Naira Dubu Dari Shida ga Zakara a bangaren Mata , na ‘yan wasan dai -dai wato ‘Single’ inji Datti.

“A bana zamu fifita bangaren matasa inda zamu yi kokarin samar dasu tun daga tushe don bunkasa gasar , wanda ko ba komai a gaba zasu samu sana’ar dogaro da kansu ko samun aikin da hukumomi ko Kamfanoni zasu basu dalilin wasan”.

Gasar ana sa ran ‘yan wasa daban -daban, kama daga ‘yan dagaji zuwa kwararru ,daga cikin Najeriya da kasashen ketare zasu halarci gasar don fafatawa.

A shekarar data gabata ta 2020, ba a samu damar gudanar da gasar ta Dala Hard Court ba, sakamakon mamayar da Annobar Cutar Corona ta yiwa Duniya a Lokacin da hakan ya kawo tsaiko a dukkanin wasanni.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!