Coronavirus
‘Yan wasa na bada gudunmowa don yakar Corona Virus
Harkokin wasanni na kara samun tsaiko da koma baya ta bangarori da dama sakamakon cutar Corona Virus, mai lakabin Covid 19.
Sai dai duk da haka ‘yan wasa na wasanni daban –daban, na ta bada gudunmowa ta kudaden agaji da kayan aiki don yakar cutar da kuma rage yaduwar ta a fadin duniya. A gasar tseren motoci na Formula, dan wasan kasar Birtaniya Lewis Hamilton, ya bayyana masu kin bin umarnin killace kai a matsayin masu son kai da rashin da’a.
Hamilton,wanda ya killace kansa, bai kuma nuna alamun cutar ba, yace lamarin ba dadi kasancewar gwamnatin kasar Ingila ta bada umarnin cewa a kauracewa shiga cunkoson al’umma.
Hamilton, ya kuma yi addu’a ga masu fama da cutar tare da yabawa likitoci, da ma’aikatan lafiya, wanda yace sune abun a yabawa kasancewar sun sadaukar da rayuwar su wajen ceto al’umma, tabbasa sune gwanaye.
Daga bangaren Tennis, dan wasa Roger Federer da matar sa Mirka sun bada gudunmowar franc din kasar Switzerland miliyan daya ga al’umma marasa galihu tare da yin kira ga sauran al’umma da su bada tasu gudunmowar.
Sakamakon barazanar cutar, kasar Switzerland, ta hana haduwar mutane guri guda da sauran harkoki har sai zuwa ranar 19 ga watan Afrilu mai kamawa.
Ko a makon da ya gabata zakaran gasar Wimbledon Simona Halep, ta sanar a shafin ta na Facebook cewar zata bada gudunmowa wajen siyan kayan da ake bukata na harkokin lafiya da suka dan ganci cutar a kasar ta , ta Romania.
Labarai masu alaka.
A bi dokokin jami’an lafiya don kare yaduwar cutar Corona -Farfesa Musa Abdulkadir Tabari
Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai
Yayin da a kwallon kafa mai horar da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola, ya bada Euro, miliyan daya don yaki da cutar, a kasar Andalus wato Spain da birnin Barcelona, in da shima dan wasa Messi ya bada a dadin hakan ga asibitoci dake Barcelona da Argentina.
Cristiano Ronaldo da wakilin sa Jorge Mendes sun bada euro miliyan daya , ga asibiti guda uku na masu lura da wanda aka killace sakamakon cutar a biranen Lisbon and Porto na kasar Portugal.
Daga bangaren damben zamani, dan wasa Anthony Joshua, ya killace kansa a gida sakamakon cutar. Zakaran duniya ajin masu nauyi har gasa biyu, ya saka hoton bidiyon sa da dan sa JJ, yana koya masa karatu, jim kadan kafin ayyana cewa Yarima Charles, mai jiran gado ya kamu da cutar.
Anthony Joshua dai ya hadu tare da yin musabiha da yarima Charles, a ranar bikin kasashen rainon Ingila ta Commonwealth da aka kammala kwanaki sha shida a baya, wanda hakan ya sa ake shakku akan lafiyar sa.
Sai dai mai magana da yawun dan wasan yace ‘dan wasan na nan a gida cikin koshin lafiya, kuma yana bin dokokin da hukuma ta saka sau da kafa.’
You must be logged in to post a comment Login