Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ba ‘yan jiharmu bane masu Corona da sukayi zanga-zanga -Gwamnan Gombe

Published

on

Gwamnan jihar Gombe yace masu dauke da cutar Corona da suka gudanar da zanga-zanga a Gombe ba ‘yan asalin jihar bane.

Kwamishinan yada labaran jihar Gombe Alhaji Ibrahim Alhasan Kwami ne ya bayyana hakan ya yin tattaunawarsa da wakilinmu Ahmada Garzali Yakubu inda yace masu zanga-zangar baki ne da suka shigo jihar Gombe daga jihohin Kano, Legas, Ogun da sauran jihohi.

Kwamishinan yace a kokarinsu na dakile yaduwar cutar Covid-19 ya sanya suke yiwa duk masu shigowa jihar Gombe gwajin cutar, wanda cikin su ne aka samu mutane 101 wadanda ke dauke da cutar Corona.

Karin labarai:

Ba shiga ba fita a Gombe daga gobe Alhamis

Gwamnatin Gombe ta yabawa wasu matasa kan COVID-19

Har ila yau, Ibrahim Kwami ya ce masu zanga-zangar sun kawo siyasa ne cikin lamarin domin su batawa gwamnatin jihar Gombe suna da kuma dakile aikin kwamitin karta kwana dake yakar cutar a jihar.

Kwamishinan ya ce babbar matsalar shi ne kasancewar masu zanga-zangar na dauke da cutar Covid-19 kuma sun shiga cikin mutane a don hakane ma sukaa dauki matakin shelantawa jama’a cewa duk wanda yayi mu’amala da mutanen to ya gaggauta killace kansa.

A karshe Ibrahim Kwami ya ce wajen da aka killace masu cutar ta Covid-19 babu wani abun more rayuwa amma yanzu gwamnati ta dauki matakan samar musu da talabijin da sauran ababen more rayuwa domin kwantar musu da hankali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!