Labarai
‘Yan wasan cikin gida zasu fara wasa a Super Eagles-Shehu Dikko
Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF)kuma shugaban hukumar shirya gasar Lig ta kasa LMC, Shehu Dikko, ya sanar da cewar sabon kwantiragin da hukumar kwallon kafa ta kasa zata baiwa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Gernot Rohr, zai tabbatar da cewa an baiwa ‘yan wasa masu taka leda a cikin gida damar bada tasu gudunmowar a cikin kungiyar.
Shehu Dikko, ya kara da cewa yanzu haka mai horar wa Gernot Rohr, zaiyi aiki kafada da kafada da mataimakan sa don kallon ‘yan wasan dake buga firimiya ta kasa da duba hazakar su.
Labarai masu alaka.
An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu
An fitar da sunayen wadan da za a karrama a bangren wasanni
Shehu Dikko, ya ce’ lokaci yayi yanzu haka da za’a takaita laruwa da ‘yan wasa masu buga wasa a kasashen ketare wanda kasar nan tayi shuhura da sunayen su, don haka yanzu za’a bada dama ga ‘yan wasan su nuna hazakar su a kungiyar ta Super Eagles’.
A baya dai hukumar kwallon kafa ta kasa ta sanar da cewar ba zata tsawaita kwantiragin mai horar wa Gernort Rohr, ba har sai ya aminta da wasu sharudda da hukumar ta gindaya masa, wanda shima a bangaren sa yace a shirye yake da karbar sharudan don cigaba da aikin tare da bunkasa harkokin kwallon kafa a kasar.
You must be logged in to post a comment Login