Labaran Wasanni
Yan wasan Najeriya 9 ba za su buga wasan Cape Verde ba -Rohr
Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles za ta buga wasan neman tikitin buga kofin Duniya da kasar Cape Verde ba tare da ‘yan wasan ta guda 9 ba.
Najeriya dai za ta buga wasan na ta ne a ranar Talata 7 ga Satumbar 2021.
Mai horar da kungiyar Gernot Rohr ne ya tabbatar da hakan a taron manema labarai da ya gudanar gabannin wasan.
Qatar 2022: Gernot Rohr ya fitar da sunayen ‘yan wasa 30 a wasan Liberia da Cape Verde
Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila ce ta haramtawa ‘yan wasan da ke wasa a kasar buga wasa a wasu kasashen da Ingila ta nuna kin gamsuwar ta sakamakon tsoran kamuwa da cutar Covid- 19 wadda kasar Cape Verde na cikin kasashen.
Sai dai mai horarwa Gernat Rohr bai ambaci ko sunayen wadanne ‘yan wasa bane, inda tuni ‘yan wasa 5 cikin 9 da ke buga wasa a kasar ingila suka bar sansanin Super Eagles bayan tashi daga karawa da kasar Liberia.
You must be logged in to post a comment Login