Labaran Wasanni
‘Yan wasan Najeriya sun kammala duk wani shiri domin tunkarar gasar cin kofin Afrika – Austin Eguavoen
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Austin Eguavoen ya ce ya yi farin ciki da ‘yan wasan da ya gayyata 28 da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON a kasar Cameroon.
Super Eagles dai za ta fafata da kasashen Masar wato (Egypt) da Sudan da kuma Guinea Bissau a rukunin da suke ciki na D.
Gasar ta shekarar 2021 ta AFCON za ta gudana daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga Fabrairun shekarar 2022 a manyan biranen kasar Kamaru 5.
Da ya ke jawabi gabanin fara gasar Eguavoen ya ce tawagar tuni ta fara shirin yadda za ta tunkari zakarun gasar har sau 7 a kasar Masar.
“Kasar Masar tawaga ce mai karfin gaske wanda hakan ya basu damar lashe gasar har sau 7, sai dai munata shirye-shirye da kuma shirin tun karar kasar,” a cewar Eguavoen yayin ganawarsa da gidan talabijin na kasa NFF
Mai shekaru 56 ya kara da cewa kungiyar na kuma shirin lashe gasar ta AFCON da tawagar ta dade bata lashe ba.
Tawagar Super Eagles dai za ta fara buga wasan farko da kasar Masar a wasan farko a ranar 11 ga wata a filin wasa na Stade Roumdé Adjia
You must be logged in to post a comment Login