Labarai
Yana da kyau manoman Dawa su kara kaimi wajen bunkasa nomanta: ICRISAT
Jigo a cibiyar binciken harkokin Noma a ƙasashe masu zafi ta ICRISAT Dakta Hakeem Ajegbe ya yi kira ga manoma da su karbi tsarin noman Dawa hannu biyu, la’akari da muhimmancinta a jikin dan Adam.
Dakta Hakeem Ajegbe ya bayyana haka yayin zantawarsa da manema labarai, biyo bayan wani sabon bincike da ya nuna muhimmancin dawa a jikin dan adam.
A nasa bangaren sabon shugaban cibiyar ta ICRISAT shiyyar Kano Dakta Angarawai Iganatious ya ce, Dawa na daga cikin sinadaran da ake amfani da ita wajen sarrafa magunguna ciki har da magani daji wato Cancer a turance.
A yayin taron an sarrafa dawa zuwa abubuwa da dama ciki har da taliya da sauransu.
Rahoton: Hafsat Abdullahi Danladi
You must be logged in to post a comment Login