Labaran Kano
Yanayin sanyi na tasiri ga rayuwar bil’adama- Musa Tanko
Wani malami daga sashen nazarin labarun kasa wato Geography na jami’ar Bayero anan Kano Malam Musa Tanko Haruna, ya bayyana bukatar dake akwai wajen mutane su kiyaye yadda suke gudanar da harkokin su na yau da kullum a lokacin yanayin sanyi.
Malam Musa Tanko Haruna ya bayyana hakan ne cikin shirin Mu leka Mu Gano na musamman, na nan tashar Freedom Radio da ya mayar da hankali kan sauyin yanayin da ake fuskanta a halin yanzu da kuma sanyi mai tsanani a nan Kano.
Ya ce shakka babu yanayin sanyi na tasiri ga yanayin rayuwar bil’adama musamman masu fama da cutuka na numfashi da dai sauran su.
Malamin ya kara da kara da cewa, tasirin na taba har yanayin muhallin da mutane ke zaune, kasancewar kai kawon mutane na raguwa duba da wasu na daukar matakin takaita zirga-zirga a waje idan bata zama dole ba.
Ta cikin shirin na Mu Leka Mu Gano da aka gabatar a tashar Freedom Radio da yammacin yau, masanin yanayin kasar ya ce ya zama wajibi mutane su maida hankali wajen kyautata muhallin su, don tabbatar da cewa yanayin bai yiwa zaman lafiyar su illa ba.
Idan ba a manta ba dai kimanin makwanni uku da suka gabata, ake fuskantar matsanancin sanyi da yanayin ya sauka a wasu lokutan har zuwa ma’aunin Selsiyas 9 zuwa 8 a cikin dare, yayin da wasu lokutan da rana akan samu yanayin ya kama daga ma’aunin Selsiyas 15 zuwa 14.
Rahotanni na nuni da cewa, mutane a wadannan yankuna namu sun shiga halin dimuwa, kasancewar da dama na ganin cewar an samu wani yanayi da ba a saba da shi.