Connect with us

Labarai

‘Yancin Mata na raguwa a Duniya – MDD 

Published

on

Rahoton Majalisar dinkin Duniya ya bayyana cewa mata a duniya suna da kashi 64 cikin 100 na ‘yancin doka idan aka kwatanta da maza. Rahoton ya ce duk da ci gaban da aka samu, har yanzu mata da ‘yan mata ba su da daidaito da maza a karkashin doka a kasashe da dama.

 

Rahoton ya kuma nuna cewa a wasu wurare dokoki suna takaita ‘yancin mata, yayin da wasu kasashe ba su da dokokin da ke tabbatar da daidaiton albashi ko kare mata daga cin zarafi. Duk da haka, an samu dan ci gaba domin kasashe da dama sun kafa dokoki kan lamarin.

 

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce tabbatar da adalci ga mata da ‘yan mata na da muhimmanci wajen gina al’umma mai adalci da ci gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!