Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Yanzu-yanzu: An kashe shugaban ƙungiyar Boko Haram ‘Shekau’ a Dajin Sambisa

Published

on

Rahotanni daga garin Maiduguri na cewa mayakan kungiyar ISWAP sun kashe jagoran ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yayin wani batakashi da su ka yi a dajin Sambia.

 

A cewar wata majiya lamarin ya faru ne a jiya laraba.

 

Majiyar ta ce dubban dubatar mayakan ISWAP ne suka shiga dajin Sambisa dauke da manyan makamai inda suka yi ta farautar jagoran na Boko Haram.

 

Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa ba mayakan na ISWAP bane suka kashe shugaban ƙungiyar ta Boko Haram shine da kansa ya yi ƙunar bakin wake ya hallaka kansa lokaci da ya fuskanci cewa mayakan na ISWAP na daf da cimmasa.

 

Har ya zuwa yanzu dai rundunar sojin kasar nan ba ta fitar da sanarwa kan wannan lamari ba

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!