Labarai
Yanzu-yanzu: Kotu ta dakatar da Anti-Corruption daga bincikar Sarkin Kano
Babbar kotun tarayya dake Kano karkashin mai shari’a lewis Alagua ta dakatar da hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano da shugaban ta Muhyi Magaji Rimingado daga binciken sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na biyu.
Cikin kunshin umarnin wanda sarkin Kano ya shigar da karar Muhuyi da hukumarsa da kwamishinan Shari’a da gwamnan Kano, Mai shari’a Alagua ya ayyana cewar kowa ya tsaya a matsayarsa yanzu magana ta dawo kotu.
Wakilinmu yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar Mai shari’a Alagua ya sanya ranar 18 mayu dan kowane bangare ya gabatar da jawabansa.
Hukumar karbar korafe-korafe ta gayyaci sarkin cewar ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tambayoyi dangane da wasu zarge-zarge a ranar litinin mai zuwa.
Kodayake yanzu maganar ta koma kotu.
Ko a watan da ya gabata ma babbar kotun tarayya mai lamba biyu ta soke wani bincike da hukumar tayi inda kotun ta ayyana cewar an tauyewa sarkin yancin da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi.
Ku kalli takardar koton a kasa:
You must be logged in to post a comment Login