Labarai
Yanzu-yanzu: Kotun ƙoli ta amince a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗi
Kotun ƙolin ƙasar nan ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.
Yayin yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar babban bankin kasa CBN ta tanada, wadda ta ce, kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.
Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.
Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin halastaccen kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.
Kotun ta kuma soke matakin gwamnatin tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.
Wasu gwamnonin ƙasar nan ne suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar tsarin sanya wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi.
You must be logged in to post a comment Login