Labaran Wasanni
Steven Gerrard ya zama sabon mai horar da Aston Villa

Labaran dake fitowa daga kasar Ingila sun tabbatar da cewar kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa , ta nada Steven Gerrard a matsayin sabon mai horar da tawagar.
Tsohon dan wasan Liverpool Gerrard , ya kasance mai horar da tawagar Rangers dake ƙasar Scotland kafin nadin nasa a Alhamis 11 ga Nuwamba 2021 , da Villa tayi.
Nadin na Gerrard na zuwa ne bayan da tawagar ta Aston Villa ta sallami mai horar da kungiyar Dean Smith a farkon makon nan.
You must be logged in to post a comment Login