Labaran Kano
Yanzu-yanzu: Yar Sarkin Kano Sanusi na daya ta rasu
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Mun sami labarin rasuwar Fulani Tafada Sanusi, matar Marigayi Mai Unguwar Mundubawa Shehu Kazaure kuma ‘Yar Marigayi Sarkin Kano Sanusi Na Daya.
Za ayi jana’izar ta a kofar kudu, Fadar mai martaba Sarkin Kano da karfe 2 na rana gobe Laraba.
Allah Yaji kanta da rahama, Ya kyauta namu zuwan.
Mun samu sanarwa daga ‘Yan Dakan Kano, Alhaji Abbas M. Dalhatu.
You must be logged in to post a comment Login