Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

‘Yar Sardaunan Sokoto Aisha Ahmadu Bello ta rasu tana da shekaru 76

Published

on

Rahotanni sun ce hajiya Aisha Ahmadu Bello wadda ita ce ‘yar Sardauna ta biyu ta rasu ne a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa tana da shekaru saba’in da shida a duniya, bayan ta yi fama da wata gajeruwar rashin lafiya.

 

Ta kuma rasu ne tabar ‘ya’ya biyar da kuma kanwarta wadda it ace ‘yar sardauna ta karshe.

 

Injiniya Aminu Nuhu wanda daya ne daga cikin makusancin marigayiyar ya tabbatarwa jaridar daily trust rasuwar marigayiyar.

 

A cewar sa ta mutu ne a yau juma’a.

 

Cikin ‘ya’yanta akwai Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba da kuma mai dakin sarkin Sudan, Shehu Malami.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!