Labarai
Labaran ƙarya da yaɗa bayanai marasa tushe sun fi rashin tsaro barazana- Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce labaran ƙarya da yaɗa bayanan da ba su da tushe sun fi matsalar rashin tsaro barazana ga zaman lafiyar al’ummar jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana haka, lokacin da ya karɓi shugabannin reshen Kaduna na Ƙungiyar ma su hulɗa da jama’a ta Najeriya NIPR.
Ya ce, yaɗa bayanan ƙarya na iya ƙara tayar da hankali da haifar da rashin yarda a tsakanin jama’a tare da kawo cikas ga ƙoƙarin da a ke yi na samar da zaman lafiya a Kaduna da sauran sassan Najeriya.
Maiyaki ya ce, gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin aiki tare da NIPR da sauran ƙungiyoyin ƙwararru wajen inganta sadarwa da kuma tallata Kaduna, musamman a fannin al’adu, zuba jari da harkar ma’adinai.
You must be logged in to post a comment Login