Labarai
Yau ɗalibai ke komawa makaranta a Kano bayan hutun Corona
Bayan kwashe kusan watanni bakwai sakamakon cutar Corona, a yau Litinin ne ɗalibai ke komawa makaranta a nan Kano.
Za a buɗe makarantu firamare dana sakandire na gwamnati da kuma masu zaman kansu cikin tsauraran matakan kariya saboda cutar Corona.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Malam Sanusi Sa’idu Ƙiru ya shaida wa Freedom Radio cewa an yi feshin kashe ƙwayoyin cututtuka a makarantu, sannan an tanadi wuraren wanke hannu, haka kuma za a raba takunkumin rufe baki da hanci a makarantu.
Kwamishinan ya ce, an raba wa ɗaliban ranakun zuwa makarantar domin kaucewa cunkoso.
A nasu ɓangaren ɗaliban jihar Kano da za su koma karatu a yau Litinin 10 ga watan Oktoba, sun bayyana farin cikinsu game da komawar tasu, inda wasu daga cikinsu ke cewa komawa makarantar zata rage musu zaman banza, inda wasu kuma ke cewa sun manta inda aka kwana.
You must be logged in to post a comment Login