Connect with us

Labarai

Yau ake sa ran APC zata fitar da jadawalin sunayen ‘yan takara a zaɓen fitar da gwani

Published

on

Yau ake sa ran jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da jadawalin sunayen mutanen da ta amince su tsaya takara a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar a wani ɓangare na cika ƙa’idar lokacin da Hukumar zaɓe INEC ta ware a gudanar da zaɓen.

 

Hakan na nufin yau ne gwamnoni 30 zuwa 31 da sanatoci 88 da ƴanmajalisar wakilai 242 da babban mai ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu, Osifo Stanley da wasu 2,620 za su san makomarsu kan ko za su samu damar yin takara a zaɓen 2027 ƙarƙashin inuwar jam’iyya mai mulki ta APC.

 

Shi ma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu da Sanata mai wakiltar Ogun ta gabas, Gbenga Daniel da tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo na daga cikin waɗanda jam’iyyar ta tantance.

 

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jam’iyyar ta tantance ƴantakara 2,980 da ke neman kujerar shugaban ƙasa sai gwamnoni 28 da sanatoci 109 da ƴanmajalisar wakilai 360 da kuma ƴanmajalisar jiha 991.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!