Connect with us

Labarai

APC ta fitar da jadawali da tsare-tsarenta na zaben 2027

Published

on

Jam’iyyar APC, ta fitar da jadawali da tsare-tsaren fitar da yan takara na zaben shekarar 2027 da ke tafe.

 

Ta cikin wata sanarwar da Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Felix Morka ya fitar a Litinin ɗin makon nan, jam’iyyar ta bayyana cewa jadawalin ya kunshi muhimman matakai da za a bi kafin gudanar da zabukan fidda gwani na jam’iyyar.

 

Jadawalin, wanda Sulaiman Muhammad Argungu, Sakatare Mai Kula da Tsare-Tsare na Kasa na jam’iyyar ya sanya wa hannu, ya bayyana lokutan tantance yan takara da sauraron korafe-korafe da kuma ranakun gudanar da zabukan fidda gwani da sharuddan sayar da fom din nuna sha’awar tsayawa takara da na neman tsayawa takara.

 

Jam’iyyar APC ta jaddada cewa za ta gudanar da zabukan fidda gwani cikin gaskiya da adalci, domin karfafa dimokuradiyyar cikin gida ta jam’iyyar tare da tabbatar da ci gaba da manufofinta na siyasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!