Labarai
Yau ne ake bikin ranar tunawa da matan karkara ta duniya – MDD
Majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar 15 ga watan Oktoban ko wace shekara don ta zama ranar tunawa da matan dake zaune a karkara, domin yin duba kan irin matsalolin da suke fuskanta tare da sama musu hanyoyin warware su.
Freedom Radio ta kai ziyara Kauyen Katsinawa da ke garin ‘Dan-Hassan a karamar hukumar Kura da ke nan Kano, tare da tattaunawa da wasu mata kan irin matsalolin da suke fuskanta.
Ko da muka ziyarci garin na Katsinawa, mun tarar da matan sun fito ɗibar ruwa, wasu kuma sun tafi gona domin noma abinda za su ci.
Matan sun bayyana cewa babban kalubalen da suke fuskanta shi ne rashin ilimi, kasancewar babu makaranta mai kyau a kauyen, kuma ko da yaransu sun je makarantar ba sa komai sai wasa, kasancewar babu malamai.
Matan sun kara da cewa a yanzu haka yawancin maza sun bar ragamar kula da yaran a hannunsu, ta yadda suke turasu birane domin aikatau da kuma almajiranci.
Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso shi ne kwamishinan raya karkara na jihar Kano, ya ce gwamnatin Jihar Kano na ba da kulawa ga matan dake karkara tare da ba su kayan haihuwa kyauta.
Taken bikin ranar matan karkara na bana shi ne mata ne ke kan gaba wajen girbe abinda da aka shuka domin ciyar da iyali.
You must be logged in to post a comment Login