Labarai
Yau Umaru Musa Yar’adua ke cika shekaru 11 da rasuwa
A irin wannan rana ta yau ce a shekarar 2010 tsohon sugaban kasar Najeriya marigayi Umaru Musa Yar’adua ya rasu.
Kafin rasuwar-sa, Malam Umaru Musa Yar’adua ya kasance shugaba da ya sha alwashi aiwatar da sabbin tsare-tsare da za su kawo ci gaban kasa.
Marigayi Umar Musa Yar’adua dai an haife shi ne a ranar 16 ga watan Augustan shekara ta 1951 a garin Katsina dake lardin arewa a waccan lokaci.
Ya kasance shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa a wani matakin da wasu ke ganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da makaman gwamnati a Najeriya.
Bayan hawan shi kan karagar mulki, shugaban ya fito da sabon salon mulki inda ya fito da manufofi bakwai da ya ke gani zai yi amfani da su domin tsallakar da kasar zuwa ga tudun mun tsira.
Kafin fara aiki marigayi Umaru Musa Yar’adua ya halarci makarantar firamare ta Rafin Kuka a 1958, inda daga bisani ya shiga makarantar firamare ta kwana ta Dutsinma a 1962.
Malam Umaru Musa Yar’adua ya kuma halarci makarantar sakandiren Keffi da jihar Nassarwa a yanzu da kuma ta Barewa da ke Zari’a kafin daga bisani ya halarci jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a.
A 1999 ne aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Katsina mukamin da ya rike har zuwa 2007 lokacin da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.
Zaben da ya zo da kalubale masu yawa, sannan tsawon wa’adin shekaru 2 da ya yi yana mulkin NAJERIYA, yayi sune a gadon asibiti sakamakon rashin lafiya da ya fama da shi.
You must be logged in to post a comment Login