Labarai
Za a ƙirga kowace ƙuri’ar da aka kaɗa a zaɓen 2027- Joash Amupitan

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a ƙidaya kowace ƙuri’ar da aka kaɗa kamar yadda ya ke a bisa doka a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Shugaban ya ce hukumar ta koyi darussa daga ƙalubalen da aka fuskanta a zaɓukan baya, kuma ta inganta shirye-shiryenta domin tabbatar da sahihin zaɓe mai cike da gaskiya da adalci.
Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da ya kai tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, inda ya yi alƙawarin cewa INEC za ta gudanar da zaɓen da zai ƙara wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa da amincewa da tsarin dimokuraɗiyya.
You must be logged in to post a comment Login