Labarai
Harin Ukraine kan jirgin Ruwan Iran ya hallaka mutum 1

Iran ta ce wani hari da Ukraine ta kai kan wani jirgin ruwanta na kasuwanci a Tekun Caspian ya haddasa fashewa da ta yi sanadin mutuwar wani ma’aikacin jirgin tare da jikkata wani.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana harin a matsayin ta’addanci da cin zarafi, tare da kiran jami’in diflomasiyyar Ukraine domin mika ƙorafi.
A nata ɓangaren, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce dakarunsa sun kai hari kan wani jirgin ruwan yaƙin Rasha da wasu jiragen da ake zargin suna ɗauke da kayan soji masu alaƙa da Iran a Tekun Caspian.
Haka kuma ya zargi Rasha da bai wa Iran bayanan tauraron ɗan adam domin taimaka mata wajen kai hare-hare a Gabas ta Tsakiya. Reuters ta ce har yanzu Ukraine ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan zargin Iran ba.
You must be logged in to post a comment Login