Connect with us

Labarai

Yan majalisar wakilai na ADC sun bukaci a sauke tare da gurfanar Farfesa Joash Amupitan

Published

on

’Yan majalisar wakilai na jam’iyyar hadaka ta ADC sun bukaci a gurfanar tare da cire shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, bisa zargin nuna bangaranci kafin zaben 2027.

 

Sun bayyana haka ne bayan taronsu na farko, inda suka ce zarge-zargen da ake yi wa shugaban hukumar, musamman batun wani asusun X da ake dangantawa da shi, na iya lalata amincewar jama’a da tsarin zabe, duk da cewa INEC ta musanta alakar sa da asusun.

 

’Yan majalisar sun kuma zargi hukumar da katsalandan a rikicin cikin gida na jam’iyyar, tare da gargadin cewa irin wadannan matakai na iya kawo cikas ga dimokuradiyya, suna mai kira ga a gudanar da bincike domin kare sahihancin zabe a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!