Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a buɗe kakar wasannin NLO ta bana a Kano

Published

on

Mahukunta shirya gasar ajin ƙwararru mataki na biyu a ƙasa wato ‘Nationwide League One NLO, sun tabbatar da jihar Kano a matsayin birnin da za a fara take gasar kakar wasannin ta bana 2023/22.

Sabon Babban jami’in yaɗa labaran gasar ta ƙasa Abdulgafar Oladimeji ne ya bayyana hakan yau Asabar a Kano ya yin ganawarsa da manema labarai.

Jami’in yaɗa labaran na NLO, ya ce za a fara gasar a ranar 04 ga watan Mayu a cibiyoyin ƙasar nan da aka ware na shiyya shiyya guda 8, inda jihar Kano take da rukuni biyu da za a fafata a gasar a filayen Sani Abacha dake Kofar Mata sai na Kano dake Sabongari.

” Ina son na tabbatar muku dacewa zaku ga sabuwar gasa da ta banbanta da sauran na baya domin wannan karo tsari take da shi na musamman”

” Bugu da ƙari an shigo da Kamfanoni da zasu dau nauyin gasar da hakan zai taka gagarumar rawa , kana a ɓangare ɗaya gasar zata samu gagarumar yayatawa daga wajen kafafen yaɗa labarai” inji Abdulgafar Oladimeji.

Daga cikin wasu daga cibiyoyin da za’a gudanar da gasar sun haɗa da , filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna sai na Zaria , kana na Pantami a jihar Gombe da na Karkanda dake Katsina , haka zalika filin wasa na Giginya dake Sokoto da Kontagora a jihar Niger ciki har da na Lafia a jihar Nassarawa sai na August 04 dake Damaturu a jihar Yobe.

Za’a fara wasan na farko a tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta matasa ta Kano Pillars wato Junior Kano Pillars , da abokiyar karawar ta ta Kwankwasiyya FC, tsohuwar tawagar Samba Kurna.

Rahoton: Aminu Halilu Tudunwada

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!