Labarai
Za a fara kwashe Yan Nijeriya daga Sudan- NEMA
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta tabbatar da cewa daga gobe Talata za ta fara kwaso ‘yan Nijeriya sama da dubu biyu da ke makale a kasar Sudan mai fama da rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.
Daraktan ayyukan na musamman a hukumar Olamide Bandele ne ya sanar da hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Channels kai tsaye a yau litinin.
Olamide Bandele ya ce yanzu haka babban Daraktan hukumar ta NEMA Mustapha Habib yana birnin Alkahira na kasar Egypt, inda suka tanadi motocin da za su kwashi ‘yan Najeriyar.
A jiya Lahadi ne dai ministan harkokin wajen kasar nan Geoffrey Onyeama ya shaidawa gidan Talabijin na Channels cewa wadanda za a kwaso sun kai dubu biyar da dari biyar, kuma kashi tamanin cikinsu dalibai ne.
You must be logged in to post a comment Login