Labarai
Za a fara sarrafa shara don bunkasa tattalin arziki a Najeriya
Gwamnatin tarraya ta amince da tsarin sarrafa shara da robobi da nufin bunkasa tattalin arziki kasa da kuma samarwa matasan kasar nan aikin yi.
Ministan muhalli Alhaji Muhammad Mahmood ne bayyana hakan a taron majalisar zartaswa ta kasa, wanda shugaban kasa Muhammdu Buhari ya jagoranta a jiya Laraba.
Alhaji Muhammad Mahood ya kuma, sabon tsarin sarrafa shara da robobin zai taimaka gaya wajen ganin tattalin arzikin kasar nan ya bunkasa, baya ga ragewa matasan kasar zaman kasha wando.
Haka zalika Alhaji Mahmood ya ce, a cikin tsarin gwamnatin tarraya za ta janyo kungiyoyin masu zaman kansa da hukumomi jihohi da kananan hukumomi da kuma ma’aikatun kasar nan, da nufin hada hannunsu don bullo da tsare-tsare bunkasa tattalalin arziki.
You must be logged in to post a comment Login