Labarai
Za a fara yiwa manoma gwajin cutar Corona a Najeriya
Gwamnatin tararraya ta kaddamar da karamin akwatin da za’a yi amfani shi wajen gano wanda ke dauke da cutar Korona da ake kira da RNASwift.
Mukadashin babban darakatan hukumar bincike kan tsirrai ta kasa farfesa Alex Akpa ya bayyana hakan inda ya ce akwatin zai taimaka wajen yiwa ‘yan Najeriya manoma da masu aikin kwadago fiye da miliyan 5 yi musu gwajin cutar COVID-19.
Acewar sa, kwararru a bangaren kimiyya na kasar nan su ka kirkiri akwatin gwaje-gwajen wanda zai sanya a rage yawan kashe kudade wajen yin gwaji.
You must be logged in to post a comment Login