Connect with us

Kiwon Lafiya

Za a fara yiwa masu Yoyon Fitsari aiki kyauta a Adamawa

Published

on

Gidauniyar tallafawa harkokin kidaya ta majalisar dinkin duniya tare da hadin gwiwar cibiyar kula da harkokin lafiya ta jami’ar garin Badin za su fara aikin yi wa masu lalurar yoyon fitsari aiki kyauta a birnin Yolan Jihar Adamawa.
Babbar jami’ar hukumar a Jihar Adamawa Mrs Tulhungu Uziel ce ta sanar da hakan yau a Yola, lokacin da take zantawa da manema labarai, tana mai cewa a gobe litinin za su fara aiwatar da aikin.
Tulhungu Uziel ta ce za su kammala aikin ne a ranar 30 ga wannan wata na satumba da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!