Labaran Wasanni
Za’a gudanar da zaben shugaban hukumar wasannin rundunar soji ta Afrika

Mataimakin daraktan wasanni a shalkwatar tsaro ta kasa, Brigadier Janar Maikano Abdullahi, na daya daga cikin ‘yan takarar dake neman kujerar shugabancin hukumar wasannin rundunar soji ta Afrika wato OSMA.
Manyan jami’an soji 4 ne daga kasashen Afrika da suka hadar da Najeriya da Algeria da Kenya da kuma Guinea Conakry ke takarar neman a zabe su don shugabancin hukumar.
Haka kuma, kasashe 51 wadanda mambobi ne na Afrika kawai ke da alhakin zaben wanda zai jagoranci hukumar ta OSMA.
Za dai a gudanar da zaben ne a babban taron hukumar a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta Internet, sakamakon annobar cutar COVID-19.
Rahotonni na cewa, wanda duk ya samu damar lashe zaben a cikin ‘yan takarar, ya zama mataimakin shugaban hukumar wasannin rundunar soji ta duniya.
You must be logged in to post a comment Login