Coronavirus
Za a samar da kotun tafi da gidanka kan Coronavirus a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa tace zata samar da kotun tafi da gidanka domin hukunta masu take dokar kulle da zaman gida da gwamnatin ta sanya a wasu sassa na jihar da aka samu bullar cutar Corona.
Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin Talatar nan a fadar gwamnatin jihar.
Wakilin Freedom Radio a Jigawa Aminu Umar Shuwajo ya rawaito mana cewa gwamna Badaru ya nuna takaicinsa kan rahotonnin da ake samu na yadda wasu al’umma ke yin ka rantsaye ga dokar.
Haka kuma gwamnan ya kara da cewa duk mutanen dake son a bude garin su daga wannan doka ta zaman gida, to ya zama tilas sai an gamsu da yadda suke bin dokar sau da kafa kafin fatan su ya cika.
Labarai masu alaka:
Covid-19: Gwamnatin Jigawa ya amince a gabatar da sallar idi
Za a tsaurara dokar kulle a Jigawa
You must be logged in to post a comment Login