Labarai
Za a samar da kotuna na musamman kan hukunta masu cin zarafi – Buhari
Gwamnatin tarayya ta fara aikin samar da Kotuna na musamman da za su hukunta masu aikata laifukan da suka shafi cin zarafin jama’a musamman fyade da makamantansu.
Ministan sjari’a kuma Atoni Janar na tarayya Abubakar Malami ne ya tabbatar da hakan yayin taro na musamman da aka gudanar da kafar intanet, kan al’amuran da suka shafi cin zarafi da kuma ayyukan ta’addanci.
Sashen yaki da miyagun kwayoyi da muggan ayyuka na majalisar dinkin duniya ne, a wani bangare na bikin ranar mata da duniya ta bana, wanda ake gudanar da taron kasa da kasa a birnin Kyoto na Japan.
Malami ya yi karatun baya kan wani kwamitin yaki da ayyukan fyade da cin zarafi da ya kafa a bara, wanda yake aiki a karkashin ministocin kasar nan.
Haka zalika Abubakar Malami ya shaida cewa gwamnatin tarayya tana iya kokarinta na ganin ta kawo karshen ayyukan ta’addanci da sace-sacen mutane don garkuwa da su a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login