Labarai
Za mu ci gaba da cafke masu talla da kalaman Batsa- Gwamnatin Kano
Hukumar fatce fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta cafke wasu masu tallar magungunan Gargajiya su goma sha biyu bisa zarginsu da laifukan yin amfani da hotuna da kalaman batsa lokacin da suke tallan magani a kasuwanni.
Shugaban hukumar Abba Almustapha, ne ya bayana hakan ga manema labarai da yammacin Larabar makon nan bayan kamo masu maganin da kayansu.
Ya kuma kara da cewa wajibi ne duk wanda zai yi tallar maganin gargajiya sai ya yi rajista da hukumar ta sahale masa bayan tantance kalaman da zai yi amfani da su yayin tallar domin tabbatar da cewa kalaman nasa ba su taba mutunci ko Addini ko kuma Al’adun jihar Kano ba.
Almustapha, ya kuma ce, hukumar za ta ci gaba da bin duk masu karya dokokin hukumar don daukar matakin doka a kansu kasancewar sun zauna da wasu cikin masu tallar maganin dan kawo karshen matsalar amfani da kalamai da hotunan da suka sabawa ka’ida.
Rahoton: Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login