Labarai
Za mu ci gaba da kyautata dangantaka da kasar Indiya – Ganduje
Gwamantin Kano ta ce zata cigaba da kyautata alakar ta da Kasar Indiya wacce aka jima ana yin ta.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke karbar bakuncin karamin jakadan Kasar Indiya a Najeria a fadar gwamnatin Kano.
Ganduje ya ce dama dai akwai kyakyawar alaka tsakanin kasar ta Indiya da Najeriya sannan yace zata cigaba da dorewa tsakanin gwamnatin Kano ta fannoni daban-daban.
Yana mai cewa, alakar zata cigaba a fannin kayayyakin amfanin noma daga kasar Indiya kasancewar manoman jihar Kano na yabawa da kayayyakin nasu.
Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, karamin jakadan na kasar Indiyar a Najeriya Abay Takur ya Kuma ce ya kawo ziyarar ne shi da tawagar sa don Kara inganta alaka da jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login