Labarai
Za mu dakatar da albashin ma’aikatan kungiyar SSANU – Buhari
Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar dakatar da albashin ma’aikatan da ba malamai ba da ke jami’o’in kasar nan sakamakon tsunduma yajin aikin da ba shi da dalili.
Ministan kwadago da samar da aikin yi Chris Ngige ne ya bayana hakan yayin zaman tattaunawa da kungiyoyin da ke yajin aikin.
Ya ce sashi na 43 na dokar kungiyar kwadago na shekarar 2004 ta bai wa gwamnati damar dakatar da albashin ma’aikata a lokacin da suke yajin aiki.
Sai dai ya gargade su da cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mutunta dokoki na tsarin kungiya musamman wajen kiran kungiyoyin don tattaunawa.
Ngige ya ce yajin aikin da kungiyar ta SSANU da NASU ke yi, ya sabawa dokokin kungiyar kwadago taa Najeriya.
Kungiyoyin biyu sun fara yajin aiki na ba-sani-ba-sabo a ranar 5 ga Fabrairu, 2021 a kan gazawar gwamnatin tarayya wajen warware matsalolin su na rashin biyansu albashi da ya kai Naira Biliyan 40, da sauran bukatu.
You must be logged in to post a comment Login