Labarai
Zamu dakatar da fasfon wadanda suka ki amincewa da gwajin Corona – Buhari
Gwamnatin tarayya tace ba dadewa ba zata dakatar da fasfon masu shiga da fice cikin kasar nan da suka ki yarda da ayi musu gwajin cutar Corona.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana haka ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, in da ya kara dacewar gwamnatin zata fitar da sunayen mutane 100 da suka kaucewa ka’idojin gwajin a jaridun kasar nan.
Boss Mustapha, yace gwamnatin zata dau matakin dakatar da fasfon masu shige da fice cikin kasar nan daga farkon shekara mai kamawa zuwa watan Yuni don ya zama izina da gargadi ga masu niyyar kin bin ka’idojin.
Sakataren gwamnatin ya tabbatar da cewar gwamnatin ta kammala shirye shirye don samar da rigakafin cutar ga al’ummar kasar nan tare da ware wasu sabbin dakunan gwaje gwaje don fuskanta tare da dakile cutar a a karo na biyu.
You must be logged in to post a comment Login