Labarai
Za mu fara aikin gyaran titin Gayawa a ƙaramar hukumar Nasarawa – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano za ta fara aikin gyaran titin Ɓul-ɓula da Gayawa a ƙaramar hukumar Nasarawa.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, lokacin da ya ke ƙaddamar da dashen bishiya a garin Gama.
Getso ya ce “tuni gwamnati ta miƙa ragamar aikin ga wani kamfani, kuma za a fara aikin bada jimawa ba, sakamakon yadda aka gano yankin na fama da zaizayar ƙasa, da sauran matsalolin muhalli”.
Ya bayyana dalilan da ya sa aka zaɓi garin Gama don dasa musu bishiyar.
Tsaftar muhalli: Za mu ɗauki matakin hukunci a kan hukumar RUWASA – Dr. Getso
“Mun zaɓi garin Gama sakamakon yadda ta ke da yawan al’umma, abinda ke haifar musu da matsanancin zafi, sannan kuma garin yana fuskantar barazanar zaizayar ƙasa da kuma ambaliyar ruwa” a cewar Getso.
Ya ƙara da cewa “A ƙalla muna sa rai za mu dasawa unguwar Gama bishiya dubu Goma, kuma muna fatan za su mayar da hankali wajen rainon su don su ci moriyar su”.
Wannan dai ya biyo bayan makon gangamin dashen bishiya da gwamnatin Kano ta ware makonni biyu a faɗin jihar.
You must be logged in to post a comment Login