Labaran Kano
Al’umma su riƙa tallafawa mabuƙata a cikin su – Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA da ta mayar da hankali wajen taimakawa mabukata don ceton rayuwar su.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin ziyarar da shugaban hukumar bada agajin gaggawa ya kai masa yau a fadarsa.
Aminu Ado Bayero ya ce masu hannu da shuni su rika bada taimakon su ga al’umma ba sai gwamnati kadai ba.
“Muna sane da yadda mabuƙata suka yawaita a cikin al’umma, a don haka muke buƙatar al’umma su shigo ciki wajen tallafawa hukumar SEMA don ƙara mata ƙarfin gwiwar tallafawa mabuƙata”.
A nasa jawabin shugaban hukumar ba da agajin gaggawar Dakta Sale Aliyu Jili ya ce sun je fadar ne domin nuna farin cikin su da irin gudunmuwa da masarautar ta ke bawa mabuƙata.
Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa za su karrama mai martaba sarkin Kano a kan irin gudunmuwar da yake bayarwa ga al’umma.
You must be logged in to post a comment Login