Labarai
Za mu gudanar da babban taron PDP kamar yadda aka tsara- Sanata Wabara

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP Sanata Adolphus Wabara, ya tabbatar da cewa taron gangamin kasa na jam’iyyar da ake ta jira zai gudana kamar yadda aka tsara, ba tare da wani jinkiri ba.
Sanata Wabara ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya gudanar da mambobin jam’iyyar, inda ya ce lokaci ya yi da PDP za ta sake daidaita lamuranta tare da farfado da cikakken tsarin shugabanci a jam’iyyar.
Haka kuma Sanata Adolphus Wabara, ya bukaci mambobin jam’iyyar ta PDP a duk faɗin Najeriya da su nuna hadin kai da biyayya domin tabbatar da nasarar taron da kuma ƙarfafa matsayin PDP a siyasar ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login