Labarai
Za mu gyara manyan asibitocin 21- Gwamnatin Sokoto

Gwamnatin jihar Sakoto, ta ce, za ta gyara manyan asibitocin jihar guda 21 domin ganin tsarinsu ya yi dai-dai da na zamani.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Faruk Abubakar, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya kuma ce, gwamnatin ta ware miliyoyin kudade da aikin zai cinye, wanda idan aka fara ba za a tsaya ba har sai an kammala ayyukan.
Dakta Faruk Umar Abubakar ya ce, a halin yanzu gwamnati ta fara aikin gyara cibiyoyin lafiya guda 125 da ake da su a jihar.
Haka kuma, ya kara da cewa, an yi hakan ne domin saukaka wa mutanen da ke yankunan Karkara na tururuwar da suke yi zuwa asibitocin da ke cikin garuruwan jihar ta Sokoto.
You must be logged in to post a comment Login