Labaran Kano
Za mu hada hannu da masu ruwa da tsaki domin kawar da ciwon suga a jihar Kano – Gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudurinta na haɗa hannu da kungiyoyin wayar da kan al’umma domin ƙara faɗakarwa kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da ciwon suga da kuma hawan jini.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya tabbatar da hakan yayin taron haɗin gwiwa da ma’aikatar lafiya ta jihar ta gudanar tare da wasu kungiyoyin lafiya, domin ƙara jaddada muhimmancin kula da lafiya da kaucewa cututtukan da ke janyo mace-mace.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa suna da shirin shiga ƙauyuka domin ƙara wayar da kan jama’a tare da ba su shawarar yadda za su kare kansu daga kamuwa da cututtuka
You must be logged in to post a comment Login