Labarai
Za mu kwato sama da miliyan 588 da aka biya likitoci ba bisa ƙa’ida ba – Chris Ngige
Gwamnatin tarayya ta ce ta gano kudi naira miliyan 588 da aka biya wasu likitoci ba bisa ka’ida ba, kuma da sannu za ta kwato su.
Ministan kwadago da samar da aikin yi Dr Chris Ngige ne ya tabbatar da hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa, inda ya ce an biya kudaden ne ga likitoci masu neman kwarewa bisa kuskure, maimakon wasu likitocin.
Dr Ngige ya ce sun gano sunayen ne bayan bincike da suka gudanar a kan likitoci dubu takwas da shugaban cibiyoyin lafiya na tarayya suka mikawa gwamnati domin wani horo da za a yi musu.
To sai dai ya ce wasu likitocin sun mayar da kudin, yayin da kuma ake shirin karbo sauran.
Game da yajin aikin da likitocin suke yi kuwa, ministan ya ce gwamnatin tarayya tana nan a kan bakanta na kin biyan likitocin da ba sa zuwa aiki, domin tsarin a a cikin dokokin kwadago na duniya.
You must be logged in to post a comment Login