ilimi
Za mu magance duk matsalolin da Dawakin Kudu ke fuskanta- Mai Rago

Majalisar Karamar hukumar Dawakin Kudu, ta ce za ta ci gaba da shiga lungu da Sako na yankunan da ke karkashinta domin magance duk wasu matsaloli da al’ummar yankunan ke fuskanta.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Sani Ahmad Mai Rago, ne ya bayyana hakan, yayin wata ziyara da al’ummar garin Dabar Kwari suka kai masa a ofishinsa.
Alhaji Sani Ahmad Mai rago ya Kara da cewa babban aikin da karamar hukumar ta Sanya a gaba, sun hada da gyara makarantun yankin da Kuma inganta fannin koyo da koyarwa.
Shugaban karamar hukumar ta Dawakin Kudu Alhaji Sani Ahmad Mai rago ya Kuma bukaci hadin kan al’ummar yankin, domin ci gaba da amfanar abubuwan more rayuwa.
A nasa jawabin Alhaji Danladi Luran, a madadin mutanen na Dabar Kwari, ya bayyana cewa yankin na su na fama da matsalar rashin makarantar Islamiyya, don haka ya bukaci shugaban karamar hukumar da ya samar musu da makarantar.
You must be logged in to post a comment Login