Ƙetare
Za mu magance matsalolin lantarki da gaggawa- Shugaba Michaël Randrianirina

Shugaban mulkin sojin Madagascar, Kanal Michaël Randrianirina, ya kai ziyarar gani da ido a karon farko a babbar tashar samar da wutar lantarki a kasar.
Shugaban ya kai ziyarar ne bisa rakiyar wakilan matasa, domin bincika manyan matsalolin da suka shafi samar da wadatacciyar wutar lantarki a faɗin ƙasar.
A cewarsa, yayin ziyarar an gano matsaloli da yawa, yana mai cewa wasu za a iya magance su cikin gaggawa, yayin da wasu kuma za a ɗauki dogon lokaci kafin gyara su, sai dai ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa don ganin matsalar wuta ta zama tarihi a ƙasar.
A juma’ar da ta gabata ne aka rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin ƙasar ta Madagascar, bayan da ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin shugaba Andry Rajoelina, wanda ƴan majalisar dokokin ƙasar suka tsige bayan tserewarsa daga ƙasar domin tsira da rayuwarsa.
You must be logged in to post a comment Login