Connect with us

Labarai

Za mu rika bibiyar ayyukan Malamai da makarantu- SUBEB

Published

on

Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano SUBEB ta ce, za ta rinka bibiyar ayyukan Malamai da makarantu dan ganin yadda ake gudanar da koyo da koyarwarwa a makarantun Kano a wani bangare na inganta ilimi.

 

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ma’aikatar ta SUBEB Balarabe Danlami Jazuli ya fitar.

 

Sanarwar ta ce kwamishina na Ɗaya a hukumar, Alhaji Wada Ibrahim Daho, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar manyan jami’an hukumar zuwa Ƙaramar Hukumar Rimin Gado domin duba yadda harkokin koyarwa da koyo ke gudana a makarantun yankin.

 

Da yake yi wa jami’an sashen ilimi na ƙaramar hukumar bayanin sakamakon ziyarar, Alhaji Wada Ibrahim Daho ya ce manufar tura manyan jami’an na SUBEB zuwa ƙaramar hukuma guda a lokaci guda ita ce gano matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban ilimi tare da samar da hanyoyin magance su.

 

Ya ƙara da cewa ayarin ya  tantance yadda harkokin koyarwa da koyo ke gudana a makarantun yankin, inda ya yaba wa malamai da shugabannin Karamar Makarantar Sakandiren Gulu bisa yadda suke gudanar da ayyukansu.

 

Sai dai ya nuna damuwa kan yadda wasu malamai a Makarantar Firamaren garin na  Gulu ke yawan makara zuwa aiki duk da kasancewarsu ‘yan asalin garin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!