Labarai
Gwamnatin Kano ta sha alwashin gudanar da bincike kan dalilan rasuwar ɗalibar St. Louis Maimuna Salisu

Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin dalilin rasuwar dalibar makarantar St. Louis, Maimuna Salisu Yaro, wadda aka fi sani da Nihal, tare da daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyayen marigayiyar domin jajanta musu bisa wannan babban rashi.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da adalci, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da bincike cikin gaskiya, adalci da kuma nuna kwarewa domin gano ainihin abin da ya faru.
Gwamnan, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama tare da bai wa iyalanta haƙurin jure wannan rashi.
Rasuwar Nihal ta jawo ce-ce-ku-ce da kiraye-kirayen gudanar da bincike mai zaman kansa bayan zarge-zargen da suka bayyana dangane da yadda lamarin ya faru, Haka kuma, rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kafa kwamitin bincike na musamman tare da hadin gwiwar ma’aikatar shari’a ta jihar domin binciken lamarin.
UAS
You must be logged in to post a comment Login