Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu rufe duk tashar da ta karya dokar mu- NBC

Published

on

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Nijeriya NBC, ta ce za ta rufe duk wata tasha da ta karya dokar hukumar.

Mai magana da yawun hukumar Mista Ekanem Antia, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar.

Ya ce, hukumar za ta rufe duk wata kafar yaɗa labarai da ta yada kalaman tunzuri yayin zaben da ke ƙaratowa.

Sanarwar ta kara da cewa, babban daraktan hukumar, Malam Balarabe Ilelah, ne ya bayar da wannan gargadi domin ankarar da kafafen yada labarai.

Haka kuma ya ƙara da cewa irin wadannan kalamai da wasu gidajen yaɗa labarai ke yi na tayar da zaune tsaye.

Hukumar ta NBC ta kuma yi gargadi ga gidajen yada labarai tana mai cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen rufewa ko kuma kwace lasisin wadanda suka karya dokar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!