Labaran Kano
Za mu tashi ‘yan kasuwa masu kasa kaya akan titi – KAROTA
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta ce babu-gudu ba ja da baya kan daukar mataki kan wadanda suka kasa kaya a kan hanya a kasuwannin jihar Kano.
Shugaban hukumar Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a ya yin da yake ganawa da ‘yan kasuwar a ofishin sa dake nan Kano.
Baffa Babba Dan gundi ya nan da ranar Laraba duk dan kusuwar da ya yi taurin kai kan kin bin umarnin hukumar na kwashe kayayyakin da ya kasa akan hanya ko titi ko kuma kafa rumfa baki daya da zumar saida kayayyaki toh babu shakka zai kuka da kan sa.
Daga cikin wuraren da abun ya shafa akwai kan titin France da Igbo Road da Murtala Muhammad Way da unguwar Fagge da Bello Road kusa da kasuwar Singa da kan titin Kantin kwari da kar kashin gada da ratso wadannan kasuwannin.da su hanzarta tashi kafin nan da ranar Laraba.
Shugaban hukumar ta KAROTA ya bayyana cewar an jima suna neman dai-daitawa da ‘yan kasuwar da su tashi daga kan hanya ko rufe rumfunan da suka bude amma sun ki ji,
Akan haka ne ya bada wa’adi daga nan zuwa ranar labara su kwashe kayayyakin da suka kasa ko kuma su fuskanci fushin hukumar.
You must be logged in to post a comment Login