Labarai
Za mu yi hadin guiwa da wani kamfanin aikin tsaftar muhalli a Kano – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta sahale ma’aikatar muhalli da hukumar kwashe shara REMASAB su yi hadin gwiwa da wani kamfani da ke aikin tsaftace muhalli, wanda zai taimaka wajen inganta harkokin tsaftar muhalli a Kano baki daya.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi, jim kadan bayan kammala zagayen duban tsaftar muhalli na karshen wata.
“A zaman majalisar zartarwa ta jihar Kano Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince ma’aikatar muhalli ta yi hadin gwiwa da kamfanin don kyautata zaftar muhalli a jihar”.
“Muna da tabbacin cewa wannan kudiri zai fara aiki a watan Mayu mai kamawa don, wanda zai ba mu damar fito da tsare-tsare masu inganci na tsaftar muhalli” a cewar kwamishinan.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, za a kaddamar da fara aikin hadaka da kamfanin ne a watan gobe, wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da ministan muhalli Mohammad Mahmood Abubakar za su kaddamar.
You must be logged in to post a comment Login